Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta cafke mutane biyar da ake zargi da hada da kuma sayar da takin zamani da maganin kashe ciyawa na bogi, tare da kwace kayayyakin hada su da dama, ciki har da injuna da buhunan taki.

A cewar sanarwar da Jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar, ya tabbatar da kama Muhammad Abubakar a bisa zargin hada maganin kashe ciyawa da taki a gidansa da ke unguwar Magaji a Bauchi. An kama shi a kasuwa dauke da buhuna shida na taki da kwalaye 46 na maganin kashe ciyawa dukkansu na bogi.

Binciken da aka gudanar ya kai ga gano buhuna na NPK da Indorama, katon-katon magunguna, da kuma kayan hada taki irin su tanda, cokula da jarkoki.
Muhammad Abubakar ya amsa laifinsa tare da bayyana wani mai Abubakar Umar daga unguwar ta su amatsayin mai taimakamashi.

A wani samame daban a ranar 14 ga Mayu, rundunar ta samu labarin wani shago a kan titin Gombe mallakin wani matashi mai suna Anas Abubakar, mai shekaru 32, inda ake hada taki na bogi. Jami’ai sun kama shi da buhuna 44 da rabi na taki, wanda ya amsa cewa ya samo daga wani Abdulrahaman Muhammad daga unguwar Bakaro.
Bincike ya nuna cewa Anas yana samun kayan hada taki daga Ziya’u Bala, wanda daga bisani ya bayyana wani wurin hada taki a Natsira, kusa da kauyen Kangare. An gano buhuna 100 da wasu tarin taki a wurin.
Karin bincike ya kai ga kama Sama’ila Abdullahi da Mujahid Abdullahi, daga Natsira da Kangere. Dukkansu sun amsa laifin su na sayarwa Abdulrahaman takin, wanda shi kuma ke mika su ga Anas.
Rundunar ta ce dukkanin wuraren hada takin an lalata su tare da kwace injunan hada kayan.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya ce rundunar za ta ci gaba da sanya ido tare da kai dauki a irin wadannan wurare da ake aikata miyagun laifuka, kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci a kotu.
Discover more from BRC Radio Bauchi
Subscribe to get the latest posts sent to your email.