Switch to Hausa

Switch Now
Education

Kungiyar tsoffin daliban makarantar sakandaren Kafin Madaki, ta shiryawa malamai da daliban makarantar wani taron bitar horawar da nufin inganta harkokin koyo da koyarwa a makarantar.

Daga Uzairu Dauda Bunga

Jagororin Kungiyar tsoffin daliban makarantar Sakandaren Kafin Madaki ta kasa(KAMOSA) sun shirya taron bita dan horar da malamai akan sabbin dabarun koyarwa da kuma fasahar koyon sana’o’i ga daliban makarantar sakandaren kwana ta ‘yan mata dake garin Kafin Madaki na jahar Bauchi.

Shugaban kungiyar na kasa Dr.Musa Mudi Jahun ne ya jagoranci shirin taron bitar horawar a harabar makarantar sakandare ta musamman dake karamar hukumar Ganjuwa ta jahar Bauchi.

Dr.Musa Mudi Jahun Wanda ya bayyana ilimi amatsayin kashin bayan cigaban kowace kasa a duniyar nan,kana ya jaddada bukatar dake a kwai ga malamai kan su Rika mu’amalantuwa da sabbin dabarun koyar da dalibai irin na zamani.

Shugaban kungiyar ta KAMOSA na kasa ya Kuma soki tsoffin dabarun koyarwa,dan haka sai ya karfafawa malaman gwiwa akan rungumar kyawawan matakan koyarwa ayayin da suke koyar da dalibai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button