Gathering of Education Secretaries of Bauchi State LGAs
Daga Hauwa Aliyu.
An kalubalanci ‘yan jarida a jahar Bauchi
dasu nemi cikakken ilimi dangane da dokokin za6e domin samun shugabanci na gari.
Babban Daraktan wata Kungiyar farar hula Mai rajin wayar da Kai kan al’amuran dokoki tare da cibiyar bunkasa al’amuran cigaba a Afirka (PAACA)Mr Ezenwa Nwagwu shine ya jefa wannan kalubale asa’ilin wani taron horarwa da aka shiryawa ma’aikatan kafofin watsa labarai,sarakuna da shugabannin addini akan dokokin za6e wanda ya gudana a Bauchi.
Yace an shirya taron ne da nufin Samar da sauyi a fagen dokokin za6e na wannan kasa ta yadda za’a samu kyakkyawan kintsi dagane da shirin za6e.
Mr Ezenwa ta bayyana cewar,manufar taron bitar itace baiwa mahalartan ilimi da kwarewar da ta dace wajen samun gamsashshiyar fahimta da kuma sadarwa akan tanade tanade da aka Samar dangane da dokokin za6e domin yada ingantattun bayanai na dokokin za6e ga al’umma.
Ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewar, shirin zai samar da sahihiyar hanya wajen cusa fahimtar muhimman tanade tanade na dokokin za6e domin samun nasarar aiwatar da shirye shiryen zabubbuka yadda ya kamata.
Shima da yake jawabi,jami’in shirye shirye na cibiyar PAACA,Mr Isiah Amonye ya bukaci ma’aikatan kafofin watsa labarai ne dasu alkinta darrusan da suka koya domin watsawa a kafofin watsa labaransu ga al’umma.
Ya kuma yi Kira ga ‘yan Najeriya dasu mayar da hankali sosai wajen fahimtar dokokin za6e domin basu damar aiwatar da ‘yancin su na dimokradiyya yadda ya kamata.
Discover more from BRC Radio Bauchi
Subscribe to get the latest posts sent to your email.