Daga Rabi’u Ishaq Muhammad
Majalisar dakoki ta jahar Bauchi ta nemi goyon baya da hadinkai daga 6angaren majalisun kananan hukumomi domin kyautata dangatakar aiki da juna domin kawo karshen matsalar nan ta sare dazuzzuka da sunan yin gawayi a jahar nan.
Shugaban kwamitin majalisar kan muhalli da gandun itatuwa Yusuf Sa’idu Ahmad shine ya bayyana hakan a yayin cigaba da rangadi da kwamitin yake yi a kananan hukumomin Ganjuwa da Dass.
Yusuf Sa’idu ya Kuma bayyana damuwarsa akan yadda ake sare bishiyoyi batare da dasa wasu ba,Yana mai bayyana cewar hakan zai janyo gurgusowar hamada da kuma lalata muhalli a akasarin yankunan jahar Bauchi.
Da yake mayar da jawabi, Shugaban kwamitin riko na majalisar karamar hukumar Ganjuwa da takwararsa na karamar hukumar Dass suka ce wannan ziyara ta zo akan ga6a tunda babban nauyi da ya rataya a wuyansu shine bijiro da manufar barin kofa a bude ga kowa dan bada shawara akan yadda za’a magance matsalolin jahar Bauchi a mataki na kananan hukumomi,suna masu jaddada bukatar hada kai da kwamitin domin cimma muradun da aka sanya a gaba.
Discover more from BRC Radio Bauchi
Subscribe to get the latest posts sent to your email.