Switch to Hausa

Switch Now
State News

Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da cigaba ta shirya wa ‘yan jarida taron horarwa na yini biyu a Bauchi

An horar da ‘yan jarida akan fasahar amfani da na’ura mai kwakwalwa a Bauchi domin inganta yadda zasu rika watsa labarai da shirye shirye cikin aminci.

Da yake jawabi a lokacin kaddamar da taron bitar na yini wand cibiyar inganta fasahar sadarwa da kuma cigaba ta shirya a sakatariyar kungiyar ‘yan jarida ta Bauchi,daya daga cikin jami’an shirin, Mubarak Shehu Dayyab ya ce manufar shirin itace nusar da ‘yan jarida wajen yin amfani da fasahohi na zamani domin inganta aiyukansu.

Ya kuma kawo wasu hanyoyi na amfani da sabbin manhajoji na zane da wallafe wallafe a shafukan sada zumunta da ‘yan jaridar zasu yi amfani da su wajen wallafa labarai cikin yanayi mai inganci,dan haka ya bukacesu kan su rungumi wannan tsari domin inganta aiyukansu.

Mubarak yace nauyin da ke kansu shine horar da ma’aikatan 6angarori daban daban na aiki kan yadda zasu rungumi sauye sauye da duniya ta kawo domin saukaka aiyukansu.

Jami’in ya kuma yi farin ciki da irin kyakkyawan hadin Kai dake wakana a tsakanin Kungiyar ‘yan jarida ta NUJ da cibiyar,ya kuma yi alkawarin dorewar dangantakar aiki a tsakanin su domin cimma muradun da aka sanya a gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button