Switch to Hausa

Switch Now
Breaking NewsNational

Shugaba majalisar dokoki na jahar Bauchi ya nemi a yi Karin haske dangan.e da aikin hako albarkatun man fetur a yankin Kolmani

Shugaban majalisar dokoki na jahar Bauchi Abubakar.Y. Sulaiman yayi Kira ga gwamnatin jahar Bauchi da ta hadakai masu ruwa da tsaki a mataki na tarayya domin maido da binciko albarkatun man fetur a yankin Kogin Kolmani na jahar Bauchi.

Shugaban majalisar yayi Kiran ne acikin wani kudiri da ya gabatar ayayin zaman majalisar dokokin.

Abubakar Sulaiman ya kuma nuna damuwarsa akan yadda aka dakatar da aikin hako albarkatun man fetur din tun lokacin da aka rantsar da shugaban kasa,Kuma babu wani kwakkwaran dalili dangane da wannan mataki.

Ya Kara da cewar,duk kuwa da irin mataki da gwamnan jaha Bala Abdulkadir Muhammad ya dauka na Samar da kyakkyawan yanayi wa aikin hako albarkatun man fetur din, to amma Kuma an dakatar da aikin batare yin wani bayani ba.

Acikin kudirin nasa,ya kuma yi Kira ga majalisun dokoki na jahohin Bauchi da Gombe kan su kafa kwamitoci na hadingwiwa da zasu ziyarci ministan albarkatun man fetur,Kamfanin NNPC da hukumar NNDC da nufin gano dalilin da ya sanya aka dakatar da aikin a yankin,da kuma neman yadda za’a gaggauta dawo da aikin yadda ya kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button