Gwamnatin jahar Bauchi ta karyata shirye shiryen shiga cikin zanga zanga na kasa baki daya da za’a fara a ranar daya zuwa ranar Sha biyar ga watan agosta.
Sakataren gwamnatin jahar Bauchi Barista Ibrahim Kashim ne ya fada hakan a lokacin wani taron manema labarai da yayi a gidan gwamnatin jahar Bauchi.
Barista Ibrahim Kashim ya jaddada cewar gwamnatin jahar Bauchi bata da wata masaniya, kuma bata maraba da duk wani nau’i na zanga zanga a jahar.
Ya kuma gargadi masu so suyi zanga zangar da suyi tsam da ransu kafin yin wani yunkuri na shirya duk wani taro a Bauchi,yana mai jaddada cewar, gwamnatin jahar bazata lamunci duk wani yunkuri na karya doka da oda ba.
Taron manema labaran ya zone a daidai wani lokaci ake watsa wasu ya madidi cewar gwamnatin jahar Bauchi ta amince zata rufe cibiyoyin Kula da kiwan lafiya a ranar da aka tsara za’a gudanar da zanga zangar.
Ibrahim Kashim ya karyata wannan ikirari,yana fadin cewar gwamnatin jahar Bauchi bata da wata masaniya ko shiga cikin wannan matsaya.
A cewar sa an kaddamar da bincike domin gano jami’in da ya watsa wadannan bayanai dan daukar mataki,ya Kuma bada tabbacin cewar dukkan cibiyoyin Kula da lafiya a matakin farko da sauran cibiyoyi na gwamnatin jahar Bauchi zasu cigaba da zama a bude,domin kuwa a cewar sa gwamnat ta himmatu domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Discover more from BRC Radio Bauchi
Subscribe to get the latest posts sent to your email.