Daga Yahuza Yahaya Doka
Malaman addinin musulunci a jahar Bauchi sun soki lamirin yar jejeniyar Samowa Mai dauke da harufan yayata auren jinsi,madigo da luwadi(LGBTQ) wacce yammacin duniya suka bullo da ita, suna masu bayyana ta amatsayin abar kyama ga dabi’ar Dan Adam da kuma addini.
Malaman addinin musuluncin sun bayyana rashin jin dadin su ne a yayin wata lacca da kungiyar dalibai musulmi ta Najeriya ta shirya a Bauchi.
Daya daga cikin malaman,Furofesa Salisu Shehu yace irin wannan yar jejeniya ta sa6awa karantarwar addinai dama al’adu na mutan kasar nan.
Furofesa Salisu Shehu wanda shine shugaban jami’ar Istiqama dake garin Sumaila na jahar Kano,ya kuma bayyana cewar ta sa6awa addinai da al’adu na ‘yan Najeriya.
Ya kuma yi Kira ga hukumomin da abin ya shafa dasu yi amfani da dokokin da ake dasu wajen soke auren jinsi a kasar nan.
Yace malaman addinin musulunci baza su yi kasa a gwiwaba wajen ilimantar da al’ummar musulmai akan hadari dake tattare da kungiyar LGBTQ ga musulunci ba.
Tun farko cikin jawabinsa, shugaban kungiyar dalibai musulmi ta Najeriya reshen jahar Bauchi Dr Adamu Muhammad Hameed yace sun shirya taron ne da nufin ankarar da malamai da matasa akan hanyoyin da za’a magance kalubale da al’ummomin musulmai suke fuskanta da kuma yadda za’a kare musulmai daga munana. Akidu.
Discover more from BRC Radio Bauchi
Subscribe to get the latest posts sent to your email.