Switch to Hausa

Switch Now
National

An bukaci ma’aikatan kafofin watsa labarai na shiyyar arewa maso gabas, dasu rika amfani da salon aikin jarida na binciken kwa kwaf domin cigaban kasa

Daga Umar Muhammad Shira

An yi Kira ga ma’aikatan kafofin watsa labarai a shiyyar arewa maso gabas dasu yi amfani da salon aikin jarida na binciken kwa kwaf domin cimma sabon zango na cigaban kasa.

Daraktan gidauniyar MacArthur a Najeriya Dr. Kole Shettima shine yayi wannan Kira asa’ilin ayyana bude wani taron bita na yini biyu da aka shiryawa ma’aikatan kafofin watsa labarai dangane da batutuwa da kuma matsaloli da ake cinkaro dasu acikin sha’anin binciken kwa kwaf da kuma tattara bayanai a cikin al’amuran aikin jarida a yankin, Wanda ya gudana a jami’ar tarayya dake Kashere na jahar Gombe.

Dr Kole yace ma’aikatan kafofin watsa labarai suna da muhimmiyar rawar takawa wajen tallafawa cigaban kasa da kuma shafe munana nan tabbai da kasar ke dasu domin amfanar ‘yan kasa baki daya.

Shima a cikin mukalar da ya gabatar, shugaban jami’ar tarayya dake Kashere, Furofesa Umar Pate, yace Najeriya amatsayinta na kasa tana fuskantar manyan kalubale wadanda suke da alaka da cin hanci da rashawa, gur6atar al’adu da dabi’u a tsakanin masu mulki da wadanda ake mulka.

Ya kuma yi Kira ga ma’aikatan kafofin watsa labarai dasuyi amfani da damarmakinsu na aiki wajen taimakawa don dakile matsalalint da suka yi kasa dabaibayi kamar su cin hanci da rashawa, rashin shugabanci na gari, yadda ake kashe makudan kudade cikin shugabanci da kuma tsarin shara’a marar kata6us.

An zakulo ma halarta taron bitar ne daga kafofin watsa labarai,kungiyoyin farar hula, malaman jami’o’i, hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da abokan jera tafiya dan kawo cigaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button