Switch to Hausa

Switch Now
Breaking NewsLatest

Hukumar Kula da al’amuran majalisar dokoki ta jahar Bauchi ta yi Kira ga gwamnatin tarayya da ta Samarwa 6angaren masu yin dokoki ‘yancin cin gashin Kansa

A wani mataki na inganta da 6angarori na gwamnati da kuma tabbatar da duga dugan 6angaren masu yin dokoki, Hukumar Kula da al’amuran majalisar dokoki ta jahar Bauchi ta yi Kira ga gwamnatin tarayya da ta Samarwa bangaren majalisar dokoki cikakken ‘yancin cin gashin Kansa.

Shugaban hukumar Kula da al’amuran majalisar dokoki ta Bauchi,Haruna Bappah Disina shine yayi wannan Kira a yayin wata ziyarar aiki da ya kaiwa kakakin majalisar dokoki na jahar Bauchi Abubakar Yakubu Sulaiman.

Ya kuma yaba da matakan samar da aiyukan cigaba da ake gudanarwa karkashin jagoranci gwamnatin Bala Muhammad, musamman ma akan kudirorin sa na aikin shimfida hanyoyi a yankunan birane da karkara na jahar Bauchi,yana Mai fadin cewar hakan Yana da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin jaha.

Yace manufar ziyarar tasa itace dan kara yaukaka danganta ta kut da kut da majalisar dokoki ta jahar da kuma tabbatar da saita al’amuran hukumar ta yadda za’a samu aikace aikace da zasu inganta tsarin 6angaren dokoki Mai nagarta.

Haruna Bappah Disina ya kuma yi amfani da wannan dama inda yayi Kira ga gwamnatin jahar da ta Samar da wadataccen kudi da sauran kayan aiki da hukumar ke bukata domin basu damar aiwatar da aiyukan su batare da wata katsalandan ba.

Da yake mayar da jawabi, shugaban majalisar dokoki ta jahar Bauchi Abubakar Yakubu Sulaiman ya bayyana a niyar majalisar dokokince wajen marawa aikace aikacen hukumar baya domin ingantuwar al’amuran ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button