Switch to Hausa

Switch Now
Politics

Jam’iyyar PDP a karamar hukumar Misau ta kammala za6en fidda gwani atsakanin ‘ya’yan ta da za’a fafata dasu a za6en kananan hukumomi dake tafe a jahar Bauchi.

Jam’iyyar PDP a karamar hukumar Misau ta kammala za6en fidda gwani a tsakanin ‘ya’yan ta, kana ta tsayar wanda zai yi wa jam’iyyar takarar shugaban karamar hukuma da kuma Kamsiloli wadanda zasu fafata a za6en kananan hukumomi dake tafe a jahar nan.

‘Yan takarar wadanda suka samu nasara karkashin cimma daidaito na baki,an gabatar dasu ga mabiya jam’iyyar sau da kafa,dattawa da manyan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar a yayin wani biki da aka gudanar a gidan shugaban masu ruwa da tsaki na jam’iyyar Alh.Muhammad Yarima.

Da yake kar6ar ‘yan takarar, shugaban kwamitin masu ruwa da tsaki Alh.Muhammad Yarima yace jam’iyyar PDP tayi amfani da salon cimma daidaiton baki a tsakanin ‘yan takarar ne saboda irin biyayya,d’a’a da mutunta juna da ake yi, kuma an kammala za6en lami lafiya.

Ya kuma yi Kira ga dukkan ‘ya’yan jam’iyyar da su bada gagarumar gudummowa domin samun nasarar jam’iyyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button