Gwamnatin Jiha zata hada kai da Hukumomin tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya.
Gwamna Bala Muhammad ya tabbatar da shirin gwamnatinsa na yin aiki tare da Hukumomin tsaro, don tabbatar da dorewar zaman lafiya da tsaro a wannan jiha.
Da yake jawabi lokacin da yake musayar yawu da mahalarta taron Kwalejin horas da sojojin sama ta Makurdi, wanda ya gudana a Zauren Majalisar zartaswa dake Gidan Gwamnati a Bauchi, Gwamna Bala ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kasance tana iya bakin kokarinta wajen bada kariya ga wannan jiha, daga ayyukan miyagun mutane.
Ya jinjina fahimtar juna ta fiskar aiki dake wanzuwa tsakanin gwamnatin jiha da Hukumomin tsaro a wannan jiha, kuma yayi alkawarin doras da goyon bayan da gwamnatin ke baiwa jami’an tsaron, don su samu sukunin gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
Da yake bayyana wa mahalartan nasarorin da gwamnatinsa ta cimma a muhimman bangarorin tattalin arziki, cikinsu har da tsaro, Gwamna Bala Muhammad ya bukaci muhimman masu ruwa da tsakin, su mara baya wa gwamnatinsa a kokarinta na raya wannan jiha yadda ya kamata.
A nasa bangaren, Kwamandan Kwalejin Air Vice Marshal Adebayo Gabriel, yace Kwalejin, wacce ita ce kololuwar Cibiyar bada horo da ilmantar da dakarun Rundunar sha’anin shugabanci, a shirye take ta bada gudumawa wajen ciyar da daukacin kasar nan gaba.