Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Tattalin Arziki

GWAMNATIN JIHA TA FARA YIN RIJISTA WA MASU TONON MA’ADINAI DA MASU SARRAFA MA’ADINAN, DA NUFIN BASU KARIYA DA TSARO WA AL’UMMA DA MUHALLIN DA AKE TONON MA’ADINAN A CIKINSU.

Gwamnatin jiha ta kaddamar da rijista wa masu tonon ma’adinai, masu sarrafawa da dillalan ma’adinan, don tabbatar da bada kariya da tsaro wa al’umma da muhalli.

Kwamishinan albarkatun karkashin kasa na Jiha Alh. Muhammad Maiwada Bello, yace daukan wannan mataki, wani kokari ne na sake farfado da sashen tonon ma’adinai da zaburar da harkokin tattalin arziki masu dorewa a wannan jiha.

A cewarsa, hakan zai taimaka wa gwamnatin jiha ta tattara sahihan bayanan masu tonon ma’adinan, kana ta adanasu cikin wani rumbu na musamman, don kariya da tsaron al’umma, muhalli da masu harkar tonon ma’adinan.

Kwamishinan ya kara da cewa, wani Kwamiti mai karfi na hadin gwiwa, wanda ya kunshi ma’aikatan da wakilan Hukumar tara kudaden shiga ta Jihar BIRS, Kwamitin kula da sha’anin tonon ma’adinai na Majalisar Dokokin jiha, K/hukumomi da sauran Hukumomin tsaro, shi ne zai sanya ido kan aikin don tabbatar da an samu cikakkiyar biyayya.

Kwamishina Muhammad Bello ya bayyana cewa aikin, wanda aka fara ran 24 ga watan Aprilun 2024, daga karfe goma na safe zuwa karfe hudu na maraice a kullu yaumin, zai kammala ran biyu ga watan gobe, a Sashen tabbatar da bin umurnin tara kudaden shiga na Ma’aikatar albarkatun karkashin kasa ta Jiha, wadda ke daura da tsohuwar Tashar Dass a Bauchi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button