Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Labaran Jiha

Gwamna Bala Muhammad ya bada umurnin kara yawan kudaden alawus-alawus da ake baiwa Sarakunan gargajiya a Jihar nan.

Gwamna Bala Muhammad ya umurci Ma’aikatar kula da harkokin K/hukumomi da Sarautun gargajiya ta Jiha, ta fara daukan matakan kara yawan kudaden alawus-alawus na sarakunan gargajiya a wannan jiha.
Gwamnan ya bayyana haka ne, lokacin da Mai Martaba Sarkin Katagum Alh. Umar Farouq, ya jagoranci masu sarautun gargajiya daga Masarautarsa, zuwa gaisuwar Sallah a Zauren Majalisar Zartaswa ta Gidan Gwamnati dake Bauchi. Yace hakan, ya zama wajibi, don cimma muradun sarakunan, ta hanyar magance matsalolin da suke fiskanta, kuma su samu damar sauke nauyin da aka dora musu, da nufin kauda hankalinsu daga ayyukan rashin gaskiya da sauran hidimomi marasa kyau.
Ya bayyana gamsuwa game da fahimtar da kyakykyawar dangantakar aiki dake wanzuwa tsakanin gwamnatinsa da sarakunan gargajiyan wannan jiha, kuma yayi alkawarin gwamnatinsa zata cigaba da mara wa masarautun gargajiya baya, don kwalliya ta biya kudin sabulu.

Tun farko, Mai Martaba Sarkin na Katagum Alh. Umar Farouq, ya yaba wa Gwamna Bala Muhammad, bisa ayyukan raya kasa da gwamnatinsa ta bijiro dasu, wanda kuma Masarautarsa ma ta shaida hakan, kuma ya sabunta goyon bayan da Masarautarsa ke baiwa gwamnatin jiha ta yau. Sannan kuma Sarkin, ya shaida wa Gwamnan, cewa Masarautarsa ta bada umurni wa dukkan masallatai dake karkashin ikonsa, su dukufa kan yin addu’o’i wa gwamnatin jiha ta yau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button