Majalisar Dokoki ta Jiha zata dora alhakin yin anfani da kadarori da dukiyar al’umma akan Hukumomin gwamnati
DAGA RABI’U ISHAQ MUHAMMAD:
Majalisar Dokoki ta Jiha zata dora alhakin yin anfani da kadarori da dukiyar al’umma akan Hukumomin gwamnati, ta hanyar bin diddigin dukkan takardun da suka shafi sarrafa kudade, cikinsu har da rahotanni.
Shugaban Kwamitin kula da dukiyar al’umma na Majalisar Hon. Mubarak Haruna ne ya bayyana haka, yayin ran gadin Kwamitin na duba ayyuka a K/hukumomi biyar da suka hada da Toro, Bauchi, Dass, Tafawa Balewa da Bogoro.
Yace Kwamitin yana da muhimmiyar rawar takawa, wajen tabbatar da ganin cewa an inganta aiki wa al’umma. Ya kuma bayyana cewa, Majalisar a shekarun baya, ta dada karfafa tasirin ayyukan Kwamitin na gudanar da ayyukan sanya ido kan abin da sashen zartaswa ke aiwatarwa.
A cewarsa, Kwamitin zaiyi aiki tare da Majalisun K/hukumomi 20 na wannan jiha, game da karfafa rikon gaskiya da amana, da nufin kara kyautata aiki a yankunan karkara.
A cikin martaninsu, Shugaban Kwamitin rikon Majalisar K/hukumar Toro Malam Danlami Abubakar, Comrade Muhammad Jibo na K/hukumar Dass, Markus Bitrus Lusa na K/hukumar Bogoro da Sama’ila Wakili na K/hukumar T/Balewa, sai Shugabar Kwamitin riko na K/hukumar Bauchi Hajia Zainab Baban-Takko, sun bada tabbacin rubanya kokarinsu na tabbatar da dorewar kyakykyawar dangantakar aiki, tsakaninsu da Majalisar Dokokin Jiha.