Gwamnatin Jiha Zata Kara Tantance Malamai da NufinIngamcin Ilimi
Gwamnatin Jiha ta sanar da shirinta na sake tantance malamana makaranta, da nufin magance matsalar durkushewar martabar ilimi a wannan jiha.
Shugaban Hukumar ilimin bai-daya ta jiha – SUBEB Alh. Adamu Muhammad Duguri ne ya sanar da haka, yayin wani taro da yayi da dukkan Sakatarorin ilimi na K/hukumomi 20 na Jiha, wadanda suka kai masa ziyarar goyon baya a Dakin taro na Hukumar dake Bauchi.
Alh. Adamu Duguri, wanda ya bayyana damuwa game da yanayin koyon karatu a makarantun Bauchi, ya jaddada niyyar gwamnati na magance matsalolin, ta hanyar tattara bayanai, da tantance matsayin ilimi a makarantun Primary da Kananan makarantun sakandare.
Ya bayyana sashen ilimi a jiha a halin da ake ciki, a matsayin abin takaici, musamman game da yadda malamai ke zuwa bakin aiki da shiga aji don koyarwa, yana mai cewa jira kawai sukeyi wata ya kare su karbi albashi, ba tare da sun tabuka wani abin kirki ga daliban ba.
Shugaban Hukumar ta SUBEB, ya ankarar da Sakatarorin ilimin game da munanan dabi’un da malaman ke aikatawa, na maida makarantu tamkar wajen kasuwanci, yana mai cewa ba za’a kara lamuntar hakan ba. Sannan ya bayyana rashin jin dadinsa yayin da ya kai ziyaran ganin yadda dalibai suka koma makaranta don fara zangon karatu na uku, yana mai gargadin dukkan masu ruwa da tsaki, musamman Sakatarorin ilimi, su kara farka daga barci, ko kuma su kuka-da-kansu.
Alh. Adamu Duguri yayi alkawarin shirin gwamnatin jiha na hukunta duk wanda ta samu na kokarin dakushe matsayin ilimi a wannan jiha, komai girman matsayinsa kuwa.