Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
Labaran Kasa

An koka game da karuwar matsalar rashin abinci mai gina jiki a tsakanin yara a Nigeria,

Kungiyar inganta abinci mai gina jiki ta Nigeria Reshen Jihar Bauchi, ta koka game da karuwar matsalar rashin abinci mai gina jiki a tsakanin yara a Nigeria, duk kuwa da nasarorin da bangarorin abokan tafiyar raya kasa suka cimma a ayyukansu.

Sakatariyar Kungiyar a Bauchi Mrs Dabis Mwalike ce ta bayyana haka, yayin wani taron manema labarai da tayi a Bauchi, don bikin cika shekaru goma da ayyukan Shirin a Bauchi.

A cewarta, karancin abinci mai gina jiki, har yanzu abin damuwa ne, bisa la’akari da barazanar da hakan keyi ga yara, yanayin lafiyar al’umma da daukacin cigaban Jihar Bauchi da Nigeria baki daya.

Mrs. Mwalike ta bayyana cewa ta hanyar kokarin wayar da kai game da abinci mai gina jiki, an samar da wani tsarin kasafin kudi ta hanyar jan hankali sa shigar da al’umma don cimma manufa, sannan an samu tallafin malaman daddini da sarakuna wajen wayar da kai, don samun nasarar aikin.

Ta kara da cewa tare da hadin gwiwar abokan tafiyar raya kasa, Kungiyar ta aiwatar da ayyukan tallafi masu muhimmanci, tana bayana cewa Kungiyar tana fiskantar matsaloli da dama, wadanda suka hada da karancin kudin gudanarwa, duk kuwa da kirkire-kirkire da dabaru da dama da ta bullo dasu, akwai kuma rashin daga darajar daukin da take samarwa zuwa mataki na gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button