Mataimakin Gwamnan jiha Alh. Muhammad Auwal Jatau, ya bidi hadin kan sashen ‘yan kasuwa a Jiha
DAGA MUSLIM LAWAL:
Mataimakin Gwamnan jiha Alh. Muhammad Auwal Jatau, ya bidi hadin kan sashen ‘yan kasuwa, wajen farfado da masana’antun da suke durkushewa, su kuma taimaka wajen samar karin harkokin kasuwanci a wannan jiha.
Yayin kaddamar da taron Hukumar Gudanar da Ofishin maida Hukumomin gwamnati zuwa hannayen ‘yan kasuwa da kawo sauye sauyen tattalin arziki, Alh. Auwal Jatau ya bayyana cewa hakan wata alama ce dake nuni da tabbatuwar cikakken tsarin maida masana’antun gwamnati hanun ‘yan kasuwa da farfado da harkokin da suka durkushe.
Ya lissafo rawar da Hukumar ke takawa ta fiskar siyasa, tattalin arziki da zamantakewa daga lokaci zuwa lokaci, don farfado da sashen tattalin arzikin wannan jiha da sanya ido kan harkokin Hukumar da bada ishara akan yadda za’a aiwatar da manufofin da suka shafi sashen.
Don haka Mataimakin Gwamnan ya tabbatar da cewa Hukumar zata mara baya wa kokarin gwamnati na samar da gurabban aiki ga matasan wannan jiha, kuma zata samar da kayayyaki da ingantatun aiki ga al’ummar jiha.
Sakataren Gwamnatin Jiha Barista Ibrahim Muhammad Kashim, wanda yayi tsokaci a madadin mambobin Hukumar, yayi alkawarin baiwa marada kunya, ta hanyar yin aiki tukuru, don cimma nasarar aikin da aka dora musu.