Koma Sashen Turanci

Koma Yanzu
IlimiLabaran Jiha

KIRAN MAIDO DA MAKARANTAR SAKANDAREN GWAMNATI TA KWANA A SADE

Daga Rabi’u Ishaq Muhammad

Dan Majalisa Mai wakiltar Mazabar Sade a Majalisar dokokin jihar Bauchi Lawal Dauda, yayi kira ga gwamnatin jihar, ta sake makarantar sakandaren gwamnati dake Sade, wacce a baya, aka maidata ta je ke-ka-dawo, ta kwana.

Lawal Dauda, ya gabatar da bukatar ce, cikin wani kuduri da ya gabatar, yayin zaman Majalisar.

A yayin gabatarwarsa, Lawal Dauda, yace an kafa makarantar ce a shekarar 1979, kuma tun wancan lokacin, tana Mazaunin makarantar kwana ce, har zuwa lokacin da Ma’aikatar ilimi ta jihar Bauchi, ta sanar da maida ita, tare da wasu makarantun a fadin jihar, zuwa na jeka-ka-dawo.

A cewar sa, wannan manufar da gwamnatin jihar Bauchi ta bullo da ita, ta haifar da koke-koke sosai daga jama’ar jiha, yana mai karawa da bukatar gwamnati ta sake tunani kan manufar.

Yace maida makarantar Sakandaren gwamnati ta Sade zuwa ta jeka-ka-dawo, ya zama abin damuwa ga mazauna yankin, yana mai jaddada cewa makarantar ta mallaki dukkan abubuwan da ake bukata don cigaba da zamewanta makarantar kwana, don kara inganta matsayin ilimin da kwazon dalibai.

Hon. Lawal Dauda ya bayyana cewa a shekarar 2016, makarantar ta lashe lambar yabo daga Babban Ofishin Hukumar shirya jarabawar kammala makarantar sakandare ta WAEC dake Lagos, a matsayin Cibiyar da tayi zarrah a Shiyyar Bauchi ta tsakiya, kuma Hukumar shirya jarabawa ta kasa – NECO ta bata damar gudanar da jarabawar ga dalibai daga wajen makarantar.

Yayin tafka muhawara kan bukatar, yan Majalisar Sa’idu Sulaiman Darazo, Garba Lawal, Bala Abdu Rishi, Musa Nakwada da Dr. Nasiru Ahmad Ala, sunyi kira ga gwamnatin jiha ta hanzarta daukan matakin sake nazari kan manufar.

A halin da ake ciki, Dan Majalisa mai wakiltar mazabar Kirfi a Majalisar Dokokin ta jiha Barista Habibu Umar, yayi kira ga gwamnatin jiha ta gina hanyar da ta tashi daga Bara zuwa Tubule ta tuke a Wanka a cikin Karamar Hukumar Kirfi, mai tsawon kilo mita 30, don ta taimaka wajen habaka harkokin kasuwanci a yankin.

 

A cewarsa, hakan ya zama wajibi, domin zai fallashi miyagun mutane da suke boyewa a yankin mai duhuwar dazuka, suna aiwatar da munanan aika-aikansu, kuma zai taimaka wajen habaka tara kudaden shiga da kusan kashi hamsin cikin dari, ga Karamar Hukumar da ma jiha baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button