Cibiyar bunkasa makaratun tsagaya dana Allo a Jihar Bauchi tare da hadin gwauiwar Ofishin Babban Mai tallafa wa Gwamna kan harkokin addini sun ziyarar wasu kananan Hukumomin a Bauchi ta tsakiyar da Kuma Arewaci.
Shugaban cibiyar Alaramma Zakari Yau Yusuf Dauduwo, yace sun ziyarci kananan Hukumomin ne domin bayyana wa Malamai da Kuma iyayen kasa tsarin da cibiyar ta dauko domin dakile matsalar ta Almajirci.
Alaramma Zakari Yau Wanda mataimakin sa Malam Bala Ahmad Limanci ya wakilce shi, ya ce halayen da wasu Malamai ke gwada wa kan amanar da aka danka musu abin duba wa ne tare da sanin tabbacin adadin yaran dake gaban Malami, ya Kuma Kara da cewa dole ne Malami yasan shiga da ficen yaran sa da Kuma tabbatar da suna ibada.
Limanci yace duk wasu matsalolin na rashin da’a akan Almajirai ake dorawa Dan haka suka fito sanar dasu tsare – tsaren da cibiyar ke Shirin gudanarwa da tallafin gwamnatin Jihar Bauchi.
Alaramma Al’amin MaiSule Zurami Wanda shine Babban Mai tallafa wa Gwamna kan harkokin addini, ya roki shugabanin kananan Hukumomin da suna Saka gamayyar Malamai a cikin hidimonsu, tare da rokon nada masu basu shawari a fannin na Addinin, sai Kuma ya Taya su murnan lashe zaben da aka gudanar kwanan da jam’iyar PDP ta lashe baki daya.
Da suke Maida jawabai Hakimin kasar Darazo Alhaji Ibrahim Babayo dana Gamawa Alhaji Abdulkadir Ibrahim Dahuwa, sun Yaba da wannan tinani da Kuma yunkuri na magance wannan bangare da akeyi wa Arewa kallon wulakancin akan sa, sai suka roki magada annabawa da suci gaba da jajircewa tare da addua’oin da suke a wannan kasa dama jihar domin samun zaman lafiya da kawar da bala’oin ambaliyar ruwa Dake wasu bangarorin Jihar.
Shugaban karamar hukumar Dambam Wanda Kuma yayi magana Amadadin zaba bun da Kansilol su Hon Yakubu Garba Tela, yayi godiya da wannan karamci sai yayi alkawarin dabbaka dukkan abubuwan da suka bukata.
Kananan Hukumomin da cibiyar ta ziyarta dai sune Ganjuwa, Darazo, Misau, Dambam, Gamawa, Zaki, Jama’are, Itas Gadau, Shira, Giade, da Kuma karamar hukumar Katagum.
Abubuwan da aka gudanar saukan karatun Al-qurani da Addua’oin domin magance Matsalolin tare da bada unurnin ci gaba da yi
A cikin Tawagar akwai Babban Mai tallafa wa Gwamna kan harkokin addini Alaramma Al’amin Mai Zurami, mataimakin shugaba Malam Bala Ahmad Limanci, mataimakin Sakatare Alaramma Isah Muhammad Tahir, Jami’in watsa labarai Sha’aya’u Abubakar Gwanki, da Kuma shugaban kungiyar na Karamar hukumar Bauchi Alaramma Musa Muhammad Khamis.