Dan majalisar dattawa Mai wakiltar maza6ar Bauchi ta kudu ya raba naira miliyan ashirin da bakwai 27 wa dalibai da malaman makarantun Tsangaya su dari hudu 400 tare da Samar masallatai kananan fitilu masu amfani da hasken rana a maza6ar sa
Daga Yahuza Yahaya Doka
Dan majalisar dattawa mai wakiltar maza6ar Bauchi ta kudu Alhaji Shehu Buba Umar ya rabar da naira dubu hamsin hamsin N50,000 ga dalibai dari biyu 200,sai kuma naira dubu talatin talatin N30,000 ga malaman makarantun Tsangaya su dari biyu a matsayin tallafi a yankin Bauchi ta kudu.
Har ila yau,Dan majalisar dattawan ya raba kananan fitilu masu amfani da hasken rana guda hamsin N50 wa masallatai hamsin N50 na kananan hukumomi shida na shiyyar Bauchi ta kudu.
Da yake mika kudaden tare da sauran kayayyaki ta hanun kungiyar Ta’awun Awareness forum,Sanata Buba ya ce yadauki wannan matakine domin sakawa kungiyar ce a bisa irin karamci da suka numa masa ta hanyar mara Masa baya da sukayi a lokacin yakin neman za6en sa.
Wanda ya samu wakilci daga Mai tallafa masa akan harkokin majalisa Mai Jama’a Mato Toro,Shehu Buba Umar yayi alkawarin cigaba da tallafawa kungiyar,kana yayi Kiran kara samun goyon baya daga 6angaren kungiyar,ya kuma bukaci masu cingajiyar tallafin dasu yi amfani dashi yadda yadda kamata.
Tunda farko cikin jawabinsa, shugaban kungiyar ta Ta’awun Awareness forum Malam Muhammad Bello Isa yace an kafa kungiyar ce da nufin Samar da kyakkyawan wakilci wa Dan majalisar dattawa Mai wakiltar maza6ar Bauchi ta kudu ta hanyar isar da aikace aikacen sa ga jama’ar sa.
A jawabansu daban daban, babban limamin massalacin juma’a na Usman Dan fodio Aminu Rabi’u da takwararsa na masallacin juma’a na Gwallaga Imam Ibrahim Idris sun yi Kira ga musulmai da su rika sanya tsoron Allah acikin al’amuran su na yau da kullum,tare da kyautata dangantakar su day Allah domin samun kyakkyawar rayuwa.